Jawabin babban sakatare:
Jawabin Dokta/ Abdullah bn Abdul Aziz Almuslih
Babban sakatare qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta Duniya.
Da sunan Allah mai Rahama mai jin qai
'yan uwana maza da mata: maziyarta wannan shafi mai albarka…
jama'an mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.. a duniya baki xaya..
gaisuwa irin ta addinin musulumci, Assalamu Alaikum Warahamatillahi Ta'ala Wa barakatuhu..bayan haka:
manazarta mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi na duniya sunyi gangami ayau da gabas da kudu suka taro a garin Ka'aba, qarqashin inuwar haramin makka mai alfarma, a zaurukan kungiyar tarayyar kasashen musulmi don a kafa wannan qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta Duniya.
Haqiqa ilimi ne. shin akwai wanda zai qi ilimi indai ba wawa ba.

Read more...

 
Allah (s.w) na cewa : " Yusuf ya kai mai gaskiya bamu fatawar shanu bakwai mai qiba suna cin bakwai busassu,  da zangeru bakwai koraye  da wasu busassu , ko zan koma ga mutane ko zasu sani* yace zaku yi noma shekaru bakwai a jere duk abin da kuka girba ku bar shi acikin zungeransa sai kaxan daga wanda zaku ci* Sannan wasu shekaru bakwai na fari zasu zo, sun cinye abin da kuka gabatar masu sai kaxan daga cikin waxanda kuka killace* sannan wani shekara zai zo mutane za su nemi gudunmuwa aciki zasu yi lallage) (yusuf 45-49)

Read more...

 
Manzo(s.a.w) ya ce: " alfasha ba za ta tava watsuwa acikin wasu jama'a ba abayyane face sai annoba da cutuka waxanda ba tava watsuwa agabaninsu ba, sun watsu acikinsu wa ". ya kuma qara cewa "zina bai tava watsuwa acikin wasu al'umma ba face mutuwa yayi yawa acikinsu' malil ya ruwaito acikin muwaxxa.

Read more...