
SIFFOFIN TEKUNA MASU ZURFI
Allah (s.w) na cewa:"ko kamar dufai acikin teku mai zurfi, wanda taguwar ruwa ta rufe shi, abisansa akwai wata taguwar,abisansa kuma akwai girgije, duffai sashinta akan sashi, har in ya fitar da hannunsa ba ya iya ganinsa , duk wanda Allah bai sanya masa haske ba ba zai tava samun haske ba." (An-nur 40).
Haqiqar ilimi:
Kundin ilimin insakwalfidiya ta Birtaniya ta bayyana cewa: da yawa daga cikin tekuna masu zurfi suna rufe ne da wasu giragizai inda suke karai mafi yawan hasken rana, kamar yadda ake iya gani ta tauraron xan Adam.. wannan hazo da yake bayyana shi yake kare hasken rana, kuma duk lokacin da ruwan yayi zurfi da yawa duhun na qara yawa, tun daga mita dari biyu har ya zuwa mita dubu, inda za a rasa ganin komai baki xaya. Faifan sesshi shine wato(secchi disk) shine injin farko da aka fara amfani dashi wurin gane dushewar haske acikin zurfin teku.