Jawabin babban sakatare:
Jawabin Dokta/ Abdullah bn Abdul Aziz Almuslih
Babban sakatare qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta Duniya.
Da sunan Allah mai Rahama mai jin qai
'yan uwana maza da mata: maziyarta wannan shafi mai albarka…
jama'an mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.. a duniya baki xaya..
gaisuwa irin ta addinin musulumci, Assalamu Alaikum Warahamatillahi Ta'ala Wa barakatuhu..bayan haka:
manazarta mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi na duniya sunyi gangami ayau da gabas da kudu suka taro a garin Ka'aba, qarqashin inuwar haramin makka mai alfarma, a zaurukan kungiyar tarayyar kasashen musulmi don a kafa wannan qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta Duniya.
Haqiqa ilimi ne. shin akwai wanda zai qi ilimi indai ba wawa ba.

Haqiqa sakankancewa ne(yaqini) shin akwai wanda zai qi yaqini, indai ba wanda ya riqi jahilci aboki ba.
Haqiqa nazari ne da duba zuwa ga ayoyi biyu masu kammala juna :ayoyin nazari da ayoyin rubuce. Ayace a duniya da dutum da rayuwa acikin tsarinta mai ban mamaki, awannan duniya mai faxi .. mai yin tasbihi ga Ubangijinsa.
Ayoyin Alqur'ani da Sunna ita ce zancenmu gameda haqiqa da ilimi acikin wannan tsari da zubi na duniya, kuma zai iya ya sauka awani zamani wanda Dan Adam ba shi da ikon da zai iya fahimtarsa ko sanin waxannan ilimomi..
Waxannan hujjoji ne da suke tabbatar da cewa wanda ya halicci wannan duniya haqiqa shine wanda ya saukar da Alqur'ani.
Sakon wannan shafi na duniya shine ya bayyana wannan haqiqani mai haske, koda yaya ya kasance don kara cigaban ilimi da kuma tabbatar da amfanin mutane afagen nazari don amfaninsu duniya mu kuma tabbatarwa da duniya cewa addinin mu addinin ilimi ne da nazari, kuma yana neman gaskiya ne yana kuma kira zuwa ga cigaban da qirqira da kuma riqo da dalilai, da kuma cigaban halara don gina rayuwar mutum mai alafarma da karamci,qarqashin adalci kuma ilimi yayi wa alumma hidima, ba masu ruguzawa ba ne, saboda haka mutane duka zau zama cikin aminci da tsaro." Lalle wannan Alqur'ani na shiryatarwa zuwa ga mafi daidaituwa,kuma yana yiwa muminai bishara waxcanda suke nagari cewa suna da lada mai girma".
Amma ku jama'a malamai manazarta da kuma jama'ar wannan shafi…
Ya ku waxanda suke da alaka da wannan shafi to naku ne kuma daga gareku yake dominku ne, kuma gaisuwa ta da sauran 'yanuwa da sauran manazarta da malamai daga qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta Duniya., kuma muna baku dukkan girmamawa saboda kune shaidun Allah da rububiyarsa da uluhiyyarsa da sunayensa da siffofinsa da ni'imominsa( Allah ya shaida cewa babu sarki sai shi haka mala'iku da ma'abuta ilimi suna tsaye da adalci, babu sarki sai shi mabuwayi mai hikima).
Wannan kungiya ta haxa gaggan malamai da manazarta masu matsayi afagen ilimi mu'ujizar Alqur'ani da Sunna, awannan fage akwai manyan masana waxanda suke da zurfin ilimi a cikin addininmu na ma'aiki (s.a.w) don kuma su kira duk wani wanda yake da iko ko baiwa ta bin wannan turba madaidaiciya da kuma bayyana gaskiya da fitar da ita da kuma fitar haqiqar da Allah(s.w) ya sanya a duniya cikin halittunsa na abinda zai amfani mutane ya kuma qarawa masu imani imani(shine wanda ya halicci maku abinda ke cikin qasa duka),(ka ce ku dubi abinda ke cikin sammai da qasa).
Haqiqa wannan qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta Duniya ta na bin manhaja na ilimi da nazarin mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi, zamu taqaicesu kamar haka:
1-sun qetare fagen hasashe da kirdade sun isa zuwa ga haqiqa wacce ba ta karvar shakku.
2-kuma an sami dalilai abayyane acikin Alqur'ni dea Sunnar manzo(s.a.w)
3- haxa tsakanin wannan kaqiqar da ma'anar nassi ta salo mai sauqi.
4 kuma wannan ma'ana ya dace da harshen larabawa, wanda Alqur'ani ya sauka da ita.
5- ba ma binciken abubuwa na gaibu wanda Allah ne ya kevantu da sanin waxannan abubuwa, kuma mu muka yi imani dasu.
6- fassara Alqur'ani da Alqur'ani sannan da Sunna ingantacciya sannan bayanan da suka inganta daga magabata na Alumma sannan ma'anar larabci da Alqur'ani ya sauka da ita.

Muna so muyi qarin bayani anan game da kokwanto da aka tada gameda fassarar kimiya- da kuma abinda ya gabata na mu'ujizar Alqur'ani da Sunna- duka suna bayani ne akan irin nazarin da ba a tantancesu ba da yadda manazarta suka yi gaggawa wurin faxin wasu ra'ayoyin ba tare da sun taka tsantsan ba, duk da cewa irin waxannan abubuwa da suka auku kaxan ne basu da yawa, saboda haka qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta Duniya duk lokacin da zata duba wani nazari takan sanya shi awurin da ya dace ta kuma faxi sharuddansu .
Lalle wahalar da ake fuskanta gameda wannan bincike har akai ga samar da waxannan bayanai na ilimi,duk ba wani abu bane alokacin da zamu ga amfanin abin yana bayyana afilin game da mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi, ya zama dole muyi nuni da wasu daga cikin su ko manazarta zasu qasa himma don gano haqiqa:
1-tasirin da wannan abu ya bari azukatan musulmi, da kuma qaruwar yaqininsu alokacin da suke ganin waxannan ayoyi da dalilai abayyane da suka zo daga harshen manzo(s.a.w), wannan yana qarfafa gwiwa wurin riqo da Alqur'ani da sunnan masu tsarki do bin shiriyarsu.
2-maida martani na ilimi mai qarfi ga masu shakka acikin gaskiyar saqon musulumcin muhammadiyya, saboda bayyana irin waxan nan bayanai na ilimi wanda manzo(s.a.w) ya bada labarinsu shekaru dubu da xori da suka gabata a lokacin da babu wani cigaban ilimin zamani da za a iya gano waxannan bayanai,to wannan kawai ya iso ya gamsar da masu adalci na malamai su san cewa Alqur'ani daga Allah yak, kuma da gasgata manzo (s.a.w)
3-raddi da kwararan dalilai da za su yi nuni da cewa addinin musulumci dinin ilimi ne – duk kuma da kiran da manzo yayi ga falalar ilimi da malamai-to ya faxi wasu kuma bayanai na ilimi na duniya da na halittu, babu kuma wanda ya iya gogesu afagage da dama acikin hadisai masu inganci akayi waxannan bayanai da ayoyi.
4-mu'ujizar fagen ilimi itace hanya mafi sauqi wurin qara himman musulmai don su cigaba da bincike na cigaban ilimi don a qara samun faxaxa fahimtar ayoyi da Hadisai.
5-kamar kuma yadda wannan fage zai zama babban qofa ta da'awa wanda zai buxe sauran qofofin na da'awa a wannan zamani da muke ciki na ilimi, wanda ke sanya jama'a da dama shiga musulumci daga yahudawa da nasara – kuma da damansu sun fara sanin musulumci ne ta hanyar wannan ilimi.
6- babu shakka komawa zuwa ga addinin musulumci ga waxanda suka rafkana ko suka gafala , ko kuma musulumtar waxanda ba musulmi ba , duka ya faru ne lokacin da musulmai suka koma ga addininsu suka yi riqo izza da karama acikin al'umma bayan wani rotse da suka samu bayan halifancin musulumci , da mamayar mulkin mallaka.
7-wannan duka na tunasar damu hadisin manzo (s.a.w) da yake cewa (wasu daga cikin al'ummata ba za su gushe ba suna yaqi akan gaskiya, suna fuskantar wanda yayi fito na fito dasu. Har sai sun yaqi na qarshensu Masihul dajal, kuma ba ruwansu da wanda ya sava masu ko ya tozartar dasu har sai al'amarin Allah ya zo) .
mu awannan shafio na duniya muna gabatar da da'awa ce ta duniya ga gaggan malamai da manazarta da masu bada mahimmanci ga mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi. Kuma muna so su taimaka mana da iliminsu da shawarwarinsu da nasihohinsu, muna fata duka za muyi ta rayya da ku awannan fage, haka kuma muna kira ga yanuwa da suke zaune a qasashen waje waxanda ba na musulmi ba su zamo masu kira na gari da hanyar amfani da wannan hanyar ta da'awa, su kuma fa'idantu da wannan shafi da nazarin da aka gabatar aciki, muna fata zamu bada gudunmuwa don bunqasa wannan shafi don cigaba amin.
Wannan kira ce daga wannan shafi ta duniya muna fata zamu sami karvuwa acikin shafuka ta duniya wasu aiki da Alqur'ani da sunna mai tsaki.
Ya 'yanuwa maza da mata ku zamo mataimaka wannan lamari .
Allah yasa mu dace.