Me ake nufi da mu'ujizar ilimi?
Mu'ujizar ilimi fuskaci ne na fuskokin mu'ujzar Alqur'ani da Sunna kuma sun qunshi:-
- mu'ujizar bayani da lugga.
- Mu'ujizar labarai(tarihi).
- Mu'ujizar shari'a.
- Mu'ujizar ilimi(kimiya).
mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi wani reshe ne na fassarar kimiyya da Alqur'ani da Sunna suka yi nuni garesu,nuni kuma abayyane acikin nassi ,gwargwadon yadda qa'idojin ilimi suka tabbatar , kuma waxannan abubuwa an tabbatar da cewa ba za a iya ganosu ba a zamanin manzo (s.a.w), abinda ke qara tabbatar da gaskiyar manzancin manzo(s.a.w) na game da abinda ya bada labarinsa daga Allah (s.w).
kafa wannan qungiya da bunqasata:
- a shekara ta 1404 aka kafa wannan qungiya ta mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi da izini daga babban majalisa ta masallatai ta duniya ataronsu na tara.
- A shekara ta 1406 hijiriyya, babban majalisar ta amince da kafa wannan qungiya ta mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi, kuma babban sakatarenta shine Sheik Abdulmajid Alzindani.. sannan qungiyar ta zavi qungiyar qasashen musulmi ta duniya dake Maka ta zama cibiyarta, kuma ta buxe rassanta acikin Saudiyya da wajenta don cimma burinta..
- A shekara ta 1423 kwamitin zartarwa ta qungiyar qasashen musulmi a zamanta na 38 ta amince da bunqasa qungiyar aka sa mata suna: qungiya ta mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta zamo daya daga cikin kwamitocin qungiyar qasashen musulmi ta duniya mai zaman kanta, kamar haka :
- qungiyar ta haxa majalisar qungiyar- kwamitin zartarwa- Babban sakatare.
- Dokta Abdallah Muslih ya riqe maqamin babban sakatare a shekara ta 1423 har ya zuwa yanzu.
Manufofin qungiyar:
Kungiyar tana aiki don cimma manufofi kamar haka:
- Sanya kai'doji da dokoki da zasu tantance ijtihadi acikin mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.
- Bayyanar da voyayyun ma'anonin ayoyin alqur'ani da hadisan manzo(s.a.w) waxanda suke da alaqa da ilimin yanayin duniya, acikin hasken tafsiri da abinda lugga ya tabbatar da manufofin shari'ar musulumci ba tare da matsawa ba.
-haxa ilimi kauni da haqiqar imani da shigar da abinda binciken ya cimma a manhajar koyarwa a dukkan kafafe.
- taimakawa wurin samar da manazarta da malamai don binciken ilimi da haqiqar duniya acikin abin da yazo a Alqur'ani da Sunna.
- fuskantar da mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi don ta zama hanyar da'awa..
-haxa qoqarin da akayi a duniya a fagen mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.

Qungiyar tana amfani da hanyoyi da suka dace da shari'ar musulumci daga ciki:
1. sanya ma'aunin binciken mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.
2. nazarin ayoyi da hadisai da suke da dangantaka da mu'ujizar ilimi.
3. nazarin binciken mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi, da kuma tankaxe shi ta hanyar shari'a, da ilimin kimiyya sannan a amince da abinda ya dace.
4. taimakawa jama'a ko mutum xaya a nazarin mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.
5. haxa qoqarin manazarta a mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.
6. bibiyar abinda malamai manazarta suka cimma a fagen ilimin kimiyya, da abinda suke rubutawa ,da watsawa na fannin mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi
7. haxa dangantaka da masana ilimin musulumci da na kimiyya na duniya musulmai da waxanda ba musulmai ba
8. saduwa da qungiyoyimasana ilimomin musulumci da na ilimin kimiyya da kuma musayar ilimi.
9. buga littafai da majallu masu alaqa da mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi
10. haxa taruka da kwasa kwasa na qarawa juna ilimi afagen mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi watsa bincike da nazarin da suka tabbata awaxansu taruka daban daban.
11. watsa bincike da nazarin da suka tabbata ta hanyoyi da suka dace da irin tunanin mutane da matsayinsu na ilimi da wayewa.
12. taimakawa masu da'awa da 'yan jaridu a duniya –jama'a ko mutane- da nazarce nazarce don suyi amfani da ita wurin aikinsu.
13. taimakekeniya da qungiyoyi dabam dabam na ilimi da kuma shirya taruka da masu nazarin mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi
14. qoqarin shigar da wannan nazarce nazarce cikin manhajar makarantu da wuraren ilimi da qungiyoyi na duniya , ta hanyar jawo hankalin waxanda abin ya shafa..
15. Karfafa gwiwar jami’oi game da ba da dame da karfafa gwiwa na karatu mai zurfi, da kuma gabatar da gudunmuwar dammar bincike game da mu’ujizar ilimi a Alkur’ani da sunna.